GASKIYA ITACE GARKUWA

A wani ƙauye mai nisa,


     mutane sun shahara da gaskiya da rikon amana. Duk wanda ya shigo ƙauyen, sai ya yi mamakin yadda kowa ke amintattu da juna.
Akwaiwani matashi mai suna Haruna. Ya tafi kasuwa a garin da ke nesa, ya manta jaka mai kudi a kan benci. Bayan awa ɗaya, ya tuna, sai ya koma da gudu. Yana isa, sai ya ga wata tsohuwa tana tsaye kusa da jakar, tana tsaron ta.
Tsohuwarta ce, “Na ga ka manta jakarka, ban motsa daga nan ba har sai ka dawo.” Haruna ya fashe da kuka, ya ce, “Wallahi, gaskiya da amana sun fi zinariya.”

Labarin ya yadu a gari. Kowa ya yaba da halayen mutanen ƙauyen. A ƙarshe, gwamnatin jihar ta zaɓi ƙauyen a matsayin misalin gaskiya da amana.


--*Darasi:*  

Idan mutane suka zauna da gaskiya da amana, zaman lafiya da ci gaba zasu tabbata. Duniya tana buƙatar mutane irin waɗanda za su tsaya da gaskiya, ko da babu mai kallo.